ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv daga nan Tehran ta nakalto Sheikh Tahir Al-Khaqaji kwamandan rundunar Hasdu mai suna ‘rundunar Imam Ali(a)’ da ke birnin Najaf yana cewa hare-hare guda biyu ne jiragen yakin suka kai, na farkon an kai shi ne da misalign karfe 3.30 na yamma sai kuma na biyu da misalign karfe 5.30 na yamma. Alkhaqiji ya kara da cewa babu wanda ya rasa ransa sanadiyyar wadanana hare hare amma sun haddasa asarar dukiyoyi masu yawa.
Rundunar kawacen wacce Amurka take jagoranta a kasar ta Iraki, da sunan yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraki da Siriya ta bada sanarwar cewa bata kai hare-hare kan wani wuri a kasar Iraki ko Siriya a cikin ‘yan kwanaki biyu da suka gabata ba.
Mayakan Hashdusha’abi dai sun taimaka kwarai wajin dakili mayakan kungiyar Daesh a kasar wacce ta kafa abinda ta kira ‘daular musulunci’ a arewacin kasar ta Iraki. Banda haka rundunar Hashdu ta sha alwashin korar sojojin Amurka daga kasar Iraki.
342/